Muna Goyon Bayan Haramta Shi’a –  Kungiyar Izala


Kungiyar Izalatul Bidi’a wa Ikamatus Sunna ta ce tana goyon bayan matakin da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka na haramta kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta ‘yan Shi’a
A karshen mako ne dai gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufai ya ayyana haramta kungiyar ‘yan Shi’ar kana ranar Asabar ya bai wa jami’an tsaro umarnin kama kakakin kungiyar Ibrahim Musa wanda ya ce, ba zai mika kansa ba, domin haramcin ya saba tsarin mulkin Nijeriya.
A yayin jin ta bakin Sheik Abdullahi Bala Lau wanda shi ne shugaban Izala ta kasa, ya yi wa BBC karin bayani akan dalilansu na goyon bayan haramta kungiyar ta Shi’a, inda ya ce akidar mabiya darikar Shi’a ta saba wa Al-kur’ani mai girma.
Sai dai kuma tuni wasu a ciki da wajen jihar Kaduna suka soma nuna damuwa dangane da matakin da gwamnatin ta dauka.
A wata hira da BBC Dokta Jibrin Ibrahim, mai sharhi akan harkokin yau da kullum ya ce kamata ya yi gwamnatin ta dauki matakan shari’a ba wai haramta wa ‘yan Shi’a gudanar da addininsu ba.
Ya kara da ce wa ya kamata gwamnatin Malam Nasiru El-Rufa’i ta sake nazari kan batun, don kauce wa tashin hankali.

You may also like