Shugaba Muhammadu Buhari yace a shirye yake ya musanya ‘ya’yan kungiyar Boko Haram dake hannunsu da ‘yan matan sakandaren Chibok da mayakan suka yi garkuwa dasu.
Buhari yace zai baiwa kungiyar damar bayyana wadanda suke so su shiga tsakani dan tattaunawa da jami’an gwamnatin dan ganin an sako ‘yan matan kusan 200 dake hannun su.
Shugaba Buhari ya sanar da hakan ne a yayin ziyararsa a kasar Kenya a yayin da yake ganawa da manema labarai.
A makon jiya iyayen ‘Yan matan na Chibok sun bukaci shugaban ya sauka daga kujerarsa idan ba zai iya ceto ‘ya’yan nasu ba.