An bayyana alfanun kokarin da wasu rukunin ‘yan kasuwa a Jihar Kano ke yi na ganin an tallafawa shirin gwamnati na kawo karshen matsalar rashin ayyukan yi a tsakanin matasa.
Wannan jawabi ya fito daga bakin shugaban rukunin kamfanonin Mansur Jogana Enterprise, Alhaji Mansur Abdulmuminu a lokacin da yake zantawa da manema labaru a ofishinsa.
Ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da daidaita farashin kayan bukatun jama’a na yau da kullum.
“Kamar yadda aka sani, wannan gari na cikin garuruwan da suke da masana’antu, amma saboda halin da kasa ke ciki yasa da yawa kamfanoni suka rufe tare da sallamar ma’aikata. Ganin haka yasa na kuduri aniyar bude wannan kamfani domin samar da hanyar da matasa za su samu hanyar cin abinci.”
Daga nan ya bayyana wa wakilinmu cewar yanzu haka akwai sama da matasa 100 da ke samun abin sawa a bakin salati a wannan wuri.
“Kuma muna gode wa Allah bisa yadda duk wanda ke sayayya a wannan wuri zai tabbatar maku da cewar farashinmu ba ya sauyawa, kuma muna kokarin ganin an saukaka wa ‘yan kasuwa musamman masu shigowa daga gabashin kasar nan, wajen samun saukin shiga dogon cunkoson ababan hawa, wanda hakan kansa wasu kwana a Kano kafin komawa garuruwansu. Amma samar da wannan kamfani ya sa yanzu jama’a daga gabashin Kano ke gudanar da sayayyarsu su koma cikin lokaci.”
Alhaji Mansur Abdulmuminu Jogana ya bayyana durkushewar kamfanoni a matsayin babbar annoba.
“Yanzu haka idan ka cire Kamfanin Mr. Lee duk sauran sun zama gawa. Hakan tasa na yi kundunbalar kafa wannan Kamfani domin taimakon al’ummarmu, musamman ganin jama’armu sun saba aikin kamfani. Na daukar wa kaina alkawarin tsayawa kan farashin gaskiya don tallfawa abokan mu’amalarmu. Sa ma da matasa dubbai ne suka rasa aikin yi sakamakon durkushewar kamfanoni. Muna kira da babbar murya da a sake duba tsarin farfado da wadannan masana’antu don gudun haihuwar da mara ido.” Inji Jogana.