Muna Tare Da Gwamna Ganduje Saboda Yayi Mana Halacci – KannywoodƘungiyar  ƴan fim magoya bayan gwamnatin jihar Kano mai suna ‘Kannywood Movement For Buhari And Ganduje sun kai ziyara fadar gwamnatin Kano a safiyar yau Alhamis domin kara karfafa dankon zumunci tsakanin Gwamnantin shugaban kasa Buhari da gwanatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje masana’antar finafinan Hausa.

A yayin jin ta bakin kakakin kungiyar, mawaki Sa’eed Nagudu ya kara da cewa “muna so mu tabbatar wa da gwamnatin jihar Kano cewq muna godiya da abubuwan alkairi da take yi wa farfajiyar finafinan Hausa.. Sannan kuma muna so mu kara tabbatar wa da gwamnati da al’umma cewa da kannywood da gwamnatin jihar Kano akwai alaka da fahimtar juna mai kyau. 

“Wannan shine dalilin ziyarar mu zuwa gidan Gwamnantin Kano duba da yadda muke bada gudunmawarmu a harkar siyasa a jahar Kano da ma kasa baki daya. Mun sami ganawa da mai vaiqa gwamnan shawara, Honarabul Aliyu Yusuf Tumfafi”.

A yayin jin ta bakin wanda ya jagoranci tawagar ‘yan fim din wajen zaman, Nura Hussein ya bayyana cewa a tarihin Kano ba a taba yin gwamnatin da ta yi ‘yam fim halarci ba kamar Ganduje, domin ya baiwa wasu abokan aikin su irin su, Rashida Adamu (Mai Sa’a), Yahanasu Sani, Isma’il Na’Abba Afakallah da sauransu mukamai.

Nura Hussein ya kara da cewa a don haka za su baiwa gwamnatin Buhari da ta Ganduje goyon baya dari bisa dari domin cimma kudirorinsu na ciyar da kasa gaba, musamman na kare dukiyar al’umma.

Taron ya samu halartar wasu daga cikin membobin da suka hada da mutane kamar Nura Husaini, Ali Gumzak, Naziru Dan Hajiya, Sa’eed Nagudu, Saleem Ahmed Saleem, Ibrahim Kast, Tahir Lawan, Garzali Miko, Shamsu Dan Iya, Bello Muhammad Bello.

Sauran sun hada da Mustapha Musty, Hafiz Ado Baba, Yakubu Husain Barrister, Tijjani Saraki, Kabir Muhammad, Ibrahim L. Ibrahim, Iliya Kefass da Abubakar Sabo Usman.

You may also like