Munja Hankalin Buhari Kan Mukaman Da Yake Bayarwa-Gwamnonin APC


Gwamnonin Jam’iyyar APC sun ja hankalin shugaba Muhammadu Buhari akan nadin mukaman gwamnati wanda suke ganin ana ba wani bangare fifiko a jihohi ko kananan hukumomi.

A lokacin da ya ke zantawa da manema labarai bayan sun gana da Buhari, Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha wanda shi ne shugaban Gwamnonin na APC, ya ce sun ba shugaban shawarwari da suka shafi mutanen da suka dace ya nada.
“Mun ba shi shawara idan za a nada mukami a duba daga ina suka fito domin a samu daidaito amma ba a zabi mutane daga bangare guda ba ko a jiha ko a karamar hukuma” a cewar Rochas.

Rochas ya ce tafiya tare da kowane bangare zai shi zai kawo ci gaban APC a siyasance.
Wannan dai na zuwa ne bayan tsohuwar mataimakiyar gwamnan Jihar filato Pauline Tallen ta yi watsi da nadin da shugaba Muhammadu Buhai ya yi mata na jakadiyar kasar a waje, tana mai cewa, babu adalci wajen raban mukaman gwamnati a jiharta.
Tallen dai ta fito bangare guda ne da Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong.
Kuma a ganawar da suka yi da Buhari a yau Litinin, Gwamna Lalong ya ce idan ana son zaman lafiya ya dace a bayar da mukaman a wani bangare na Jihar.
A makon jiya ne shugaba Buhari ya aike da sunayen mutane 46 zuwa majalisar dattawa don tantance su a matsayin jakadun Nijeriya a kasashen waje.
A kwanan baya ne kuma uwar gidan Shugaban kasa Aisha Buhari ta fito tana sukar gwamnatin mijinta musamman yadda ake tafiya da wadanda ba a yi wahala da su ba a yakin neman zaben Jam’iyyar APC.

You may also like