Mushaƙata… KANIN LABARAI 



1- Kimanin Dalibai 10,000 ne suka zo yin karatun digiri a kan harshen larabci daga kasar Misira a makarantar koyan Shari’ah Ta Malam Aminu Kano.

2- Matar Shugaban Kasar Faransa da Iyalanta ne suka zo yin sayayyar kayan shafe-shafe a kantin Dan-Jummai dake kasuwar Kurmi a Kano.

3- An cafke wani baturen kasar Amurka sakamakon shigo da hodar Iblis a filin sauka da tashin Jiragen sama na karamar Hukumar Gwale.

4- Kamfanin kera matoci na Bature and Gwarjo Motors dake Tokarawa yayi cinikin sama da Naira Biliyan 900 daga kasashen Turai da Asiya.

5- Dakta Ahmad Abba ne ya jagoranci yiwa Firaministan Burtaniya tiyata a makogaransa a asibitin Murtala dake kano.

6- Za’a gudanar da taron kasashe masu karfin tattalin arziki a sansanin shakatawa na Hills and valley dake karamar hukumar Dawakin Kudun jihar Kano. 

7- kasar Indiya tana neman Rancen Dala Miliyan 500 a bankin Madobi Community Bank dan inganta noman Gahawa.

8- Jaridar Arewa24 News ce jaridar da aka fi karantawa a duniya.

9- Kulab din Kano Pillars ya lallasa takwaransa na Real Madrid a filin wasa na Santiago da ci-uku da nema.

10- Kananan Hukumomin Kura da garun Malam ne zasu dauki nauyin gasar cin kofin duniya na shekara mai zuwa. 

Wadannan sune irin labaran da muke fatan gani a Najeriya nan gaba Insha Allaah……..
Idan kuna da naku kuma ku ƙara dan mu farantawa juna rai

You may also like