Shugabanni Al’ummar Musulmin Amurka sun shigar da karar shugaban kasar Donald Trump a gaban kotu saboda abin da suka kira dokar da za ta hana mabiya addinin Islama shiga cikin kasar.
Nihad Awad, daraktan kungiyar Musulmin na daga cikin mutane 26 da suka shigar da karar, wadda suke cewa tana kalubalantar dokar da za ta hana Musulmi zuwa Amurka.
Awad ya ce, wannan matakin ba zai tabbatar da tsaro a dukkanin Amurka ba, face jefa fargaba a zukatan al’umma.
Lauyoyin Amurka sun ce, matakin na Trump ya saba wa sashen kundin tsarin mulkin kasar da ya bukaci kare tare da bai wa jama’a damar gudanar da addininsu.
Shugaba Doland Trump a wata hira da ya yi, ya ce suna taimaka wa al’ummar Kiristocin da ake musguna musu a wasu kasahsen Musulmai ne.
Kasashen Musulmi 7 da Trump ya hana shiga Amurka, sun hada da Syria da Iraqi da Iran da Somalia da Libya da Sudan da Yemen.