Musulmin Amurka Na Nuna Damuwa Kan Zaben Trump


 

 

Mabiya addinin muslunci a kasar da dama suna nuna damuwa da fargaba kan zaben Donald Trump a matsayin shugaban kasar.

Shafin yada labarai na Fortune ya habarta cewa, musulmi a Amurka suna nuna damuwa kan zaben Trump sakamakon kalaman kin jinin muslunci da ya rika furtawa a baya.

Da dama daga cikin musulmin da suka bayyana ra’ayoyinsu a shafukan sadarwa na Twitter suna cikin damuwa matuka, musamman ganin cewa Donald Trump mutum ne wanda ba ya boye maitarsa wajen nuna kiyayyarsa ga musulmi da kuma da kuma baki wadanda ba ‘yan asalin kasar Amurka.

Duk kuwa da cewa wasu na da ra’ayin cewa a ba shi lokaci domin ganin kamun ludayinsa, domin sau da yawa dan takara kan fadi maganganu domin burge su da ke da wani ra’ayi domin neman samun kuri’unsu, amma bayan lashe zabe, lamurra kan canja.

Tun bayan sanar da cewa Trump ne ya lashe zaben shugaban kasar Amurka, har yanzu ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar kin amincewa da shi a jahohi daban-daban na kasar.

You may also like