Wasu alkalumma na gwamnatin kasar Italiya sun yi nuni da cewa, addinin muslunci shi ne addini na biyu da ke yaduwa a cikin kasar, domin kuwa fiye da kashi 34 cikin dari na ‘yan kasashen waje da ke zaune a kasar musulmi ne.
Jaridar Press Info ta kasar Faransa ta nakalto daga jami’an gwamnatin kasar Italiya cewa yanzu haka akwai ‘yan kasashen ketare da suke zaune a kasar da adadinsu ya kai miliyan 2.4, kuma kimanin dubu 820 musulmi ne.
Rahoton ya ce musulmi suna da hannu a cikin harkokin sana’oi na cikin gidan kasar ta Italiya, domin kuwa kusan kashi 4 zuwa 5 na abubuwan da ake sana’antawa a cikin kasar suna da alaka da musulmi.
Haka nan kuma a halin yanzu akwai masallatai kimanin 700 mallakin musulmi, baya ga cibiyoyi daban-daban na addinin muslunci, amma kuma duk da hakan addinin muslunci baya daga cikin addinan da aka amince da su a hukumance a kasar, sakamakon yadda wasu jam’iyyun siyasa masu ra’ayin ‘yan mazan jiya suke nuna adawa kan hakan.
Daga cikin wadanda suke nuna amincewar da su hakan har da daya daga cikin manyan malaman majami’u Katolika na kasar Carlo Libarty, wanda ke cewa mai yiwuwa nan da shekaru 10 nahiyar turai ta zama ta musulmi, sakamakon yadda musulmi suke ta kara yawa a cikin kasashen turai.