Mutane 1000 sun shaki iska mai guba a Mosul


 

Fararen hula biyu sun rasa rayukansu, yayinda wasu dubu daya kuma ke karbar magani, sakamakon matsalar da suke fuskanta yayin numfashi, bayan shakar sinadarin Sulphur mai guba a birnin Mosul.

Shaidun gani da ido, hadi da Jami’an Amurka, sun ce fararen hular sun ga wannan tasku ne, bayan da mayakan ISIL suka kone wata babbar cibiyar adana sinadarin na Sulphur, da ke kudancin Mosul.

Darakatan wani babban asibiti da ke Qayyara, inda aka kwantar da mafi yawan masu fama da matsalar numfashin, Abdul Salam Jabbouri, ya ce kawo yanzu ba’a samu karuwar hasarar rai ba, sai dai marasa lafiyar suna jin jiki.

Kimanin sojoji 30,000 da suka kunshi na Iraqi, mayakan Kurdawa na Peshmerga, bangaren ‘yan Sunni dana Shi’a ne suka kaddamar da hari kan birnin na Mosul da nufin murkushe mayakan ISIL, wadanda ke da mayaka 6000 a cikin birnin.

You may also like