Mutane 13 Za Su Bayar da Shaida Akan Patience Jonathan a Kotu


patience1

 

Mutane 13 aka ware wadanda za su bayarda sheda cewa matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Patience Jonathan ta mallaki asusunan banki guda 4 dauke da makudan kudade.

A bisa haka ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ta ce ta karfafa tsaro akan wadannan mutane wadanda za su bayarda sheda akan yadda aka bude asusunan banki masu amfani da katin Visa Platinum Credit Card.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon mai tamakawa shugaba Goodluck Jonathan na Musamman Dr Dudafa Waripamo-Owei Emmanuel wanda shima ake tuhuma, shi ya taimakawa Patience wajen bude asusunan,.

Jaridar The Nation ta rahoto majiya daga hukumar ta EFCC na cewa “Mun kammala duk wani shirye shirye game da sauraran kara a kan yadda aka bude asusunan bankin wa Patience Jonathan, kuma mun tattara shaidu guda 13 tare da hujjojinmu, domin mu nuna cewa mun yi binciken mu da kyau”

Karanta Wannan: Patience Jonathan ta Baiwa EFCC Makonni 2 ta Sakar Mata da Kudadenta, Ko Kuma…

Ya kara da cewa ” jami’in da ke kula da asusunan zai bayyanawa kotu irin kudaden da suka shigo asusun da kuma yadda matar tshohon shugaban kasar ta gudanar da su.

Ya kuma ce ya na kyautata zaton cewa ‘yan Nijeriya ba su ji komai ba ma tukun game da wannan batu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like