Mutane 14 Ne Suka Mutu A Suleja Sakamakon Ambaliyar Ruwa


Hoto:thecable.ng

Mutane 14 ake zaton sun mutu bayan da wani mamakon ruwan sama ya haifar da ambaliyar ruwa a garin Suleja dake jihar Neja.

 Ruwan ya fara ne a ranar Asabar, ya kuma kare a ranar Lahadi. 

Lamarin yafaru ne unguwannin Banki-iku da kuma Chanchia dake karamar hukumar ta Suleja. 

Ruwan ya  lalata dukiya ta miliyoyin naira , yayin da gidaje da dama suka nutse a ruwa. 

Iyalai biyu ne suka rasa mutane 8 da kuma 6 kowannensu. 

Mutanen gari da suka iya ruwa sune suka fara aikin ceto mutane kafin jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA su iso. 

Akwai yiyuwar adadin wadanda suka mutu su karu saboda wasu iyalai da dama  har yanzu basu ga yan uwansu.

Shugaban karamar Hukumar Suleja, Abdullahi Maje,ya tabbatar da bacewar mutane 10,yayin da aka gano gawar mutane biyu a cikin ruwan a ranar Lahadi.

 Maje, yakuma ce gidaje 100 anbaliyar ruwan ta shafa, yakara da cewa gidaje takwas ruwan yayi awon gaba dasu biyo bayan ruwan da aka shafe awanni goma anayi. 

 Shedun gani da ido sunce ana zaton wasu mutane 8 yan gida daya sun rasa rayukansu a anbaliyar ruwan. 

Mai gidan ya samu nasarar tsira da ransa,amma matansa biyu da kuma yayansa shida duka sun mutu a ruwan. 

Muhammad Muhammad shine jami’in yan sanda dake kula da yankin na Suleja, yace bazai iya tabbatar da adadin wadanda suka rasa rayukansu ba, amma yace tuni jami’an yan sanda suka ziyarci wuraren da anbaliyar ta shafa. 

“Anbaliyar ta shafi gidajen da aka gina a hanyar ruwa, gidaje da yawa ne suka lalace, yayin da mutanen da ba asan adadinsu ba suka rasa rayukansu,”yace. 

” Yan sanda suna samar da tsaro a wuraren saboda kar bata gari suyi amfani da wannan damar wajen satar kayayyakin mutane musamman wadanda aka ajiye a waje.”

Isiaka Dikko, shaidar gani da ido yace yawancin wadanda suka mutu sun mutu ne saboda baza a iya cetonsu ba a lokacin da abin yafaru. 

You may also like