Mutane 15 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa


Aƙalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu ranar Asabar  lokacin da wata motar ɗaukar yashi tayi tawo mugama da wata karamar mota ƙirar Golf.

Hatsarin yafaru ne a Garin Ciroma wani kauye dake karamar hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa.

Motar ƙirar Golf mai cin mutane 7 dake da rijistar namba AA 664 DRA, amma an makareta da mutane 15.

 An ce suna kan hanyarsu ta dawowa daga Gwaram  kuma sun nufi wani ƙauye dake ƙaramar hukumar Gwiwa lokacin da hatsarin yafaru.

Audu Daurawa, mai riƙon muƙamin shugabancin Karamar Hukumar Gwiwa ya tabbatar da cewa dukkanin mutanen sun fito ne daga ƙaramar hukumar sa.

Hatsarin na ranar Asabar ya faru  kasa da wata ɗaya bayan da wani direba dake sharara gudu  ya buge wasu mutane 7 har lahira.

Mai magana da yawun rundunar yan’sanda ta jihar DSP Abdu Jinjiri ya tabbatar da faruwar hatsarin.

You may also like