
Hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta kasa FRSC ta tabbatar da mutuwar aƙalla mutane 15 da kuma wasu biyar da suka samu mummunan rauni a wani hatsarin mota da rutsa da su akan hanyar Kogi zuwa Abuja.
Kamfanin Dillancim Labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa hatsarin ya faru ne bayan da wata mota ƙirar J-5 Boxer tayi tawo mu gama da wata tankar mai a wajen Koton-Karfe akan hanyar Abuja-Lokoja da misalin karfe 07:00 na safe.
Stephen Dawulung kwamandan hukumar FRSC shiyar jihar Kogi wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce an garzaya da wadanda suka jikkata ya zuwa Asibitin Ideal dake Koton Karfe domin samun kulawar gaggawa.
Dawulung ya ce an kai gawarwakin waɗanda suka mutu ya zuwa Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya dake Lokoja.