Yan sanda a jihar Anambra, sun bayyana cewa mutane 16 aka kashe a wani fadan bindiga tsakanin wasu kungiyoyin asiri biyu da basa ga maciji da juna cikin makonni biyu a Awka babban birnin jihar Anambra.
Haka kuma mutane 36 aka kama da ake zarginsu da kasancewa ya’yan kungiyar dake da hannu a rikicin.
Kwamishinan yan sandan jihar, Garba Umar, shine ya bayyana haka a hedikwatar rundunar dake Awka, lokacin da yake nunawa manema labarai mutanen.
Ya koka kan yadda ake samun karuwar rikice-rikice dake da alaka da kungiyoyin asiri a Awka.Ya ce yana fargbar cewa furucin da wani da ake zargi ya yi cewa kaso 90 na matasan dake Awka da suka hada dalibai, masu sana’o’in hannu da sauransu duk yan kungiyar asiri ne da kamshin gaskiya a ciki.
Kwamishinan ya yi kira ga iyaye da su taka rawarsu ta hanyar tsawatarwa yaransu domin rundunar za ta fara gurfanar da su a gaban kotu kan zargin aikata kisan kai.
Kungiyoyin biyu masu suna Black Axe da Vikings sun shafe makonni biyu suna rikici da juna na neman iko da ya jawo asarar rayukan ya’yan kungiyoyin da dama.