Mutane 19 aka kashe sakamakon hari da wuka a Japan


579740d815af1

Mutane 19 ne suka mutu sakamakon hari da wuka da aka kai a garin Sagamihara da ke kusa da Tokyo babban birnin kasar Japan.

Maharin da ya shiga wata cibiyar kula da gajiyayyu ya jikkata mutane 26.

Mahukunta sun bayyana cewa, 20 daga cikin wadanda aka jikkata na cikin halin rai mutu kwakwai.

Maharin mai shekaru 26 ya taba aiki a gidan kula da gajiyayyun.

Tuni aka fara bincike game da lamarin.

You may also like