Mutane 19 Sun Mutu A Fadan Da Ake Yi Da Kungiyoyi Masu Alaka ISIL A Kasar PhilippinesMasu rike da makamai na can na gwabza fada da dakarun gwamnati a titunan dake garuruwan tsibirin  Mindanao dake kudancin kasar Philippines.

Kimanin fararen hula 19 ne suka rasa rayukansu a ranar Lahadin data gabata, wannan yakawo adadin mutanen da hukumomi suka bayyana mutuwarsu zuwa mutane 100, a rikicin da aka shafe mako guda ana gwabzawa.

Tuni shugaban kasar, Rodrigo Duterte, ya bada umarnin kara tura jami’an soja zuwa yankin domin maganin abin da yakira barazana daga kungiyoyi masu alaka da ISIS.

Jami’an tsaro na kokarin fatattakar yan kungiyar Maute  da kuma na Abu Sayyaf wadanda dukansu sunyi mubaya’a ga kungiyar ta ISIS. 

Hukumomi sunce mayakan sun kashe mutane farar hula 19 a Marawi wani birni dake cike da musulmai. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like