Mutane 2000 ne suka rasa muhallinsu bayan harin da aka kai kauyen Gwaska dake jihar Kaduna


Harin ranar 6 ga watan Mayu da ya jawo asarar rayukan mutane 71 a kauyen Gwaska dake karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, ya kuma raba kusan mutane 2000 da muhallinsu.

Wani jami’in hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kaduna SEMA da ya nemi a boye sunansa ya tabbatarwa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN yawan adadin mutanen.

Ya ce hukumar ta ranto kudi inda ta sayi kayan agaji da suka hada da buhunan shinkafa, manja dana kuli, taliya nau’in indomie, da kuma katifu inda aka rabawa mutanen a ranar Alhamis.

Jami’in ya ce an mika kayayyakin tallafin ga shugaban riko na karamar hukumar, Abdullahi Murtala domin rabawa ga mutanen da suke samun mafaka a wata makarantar firamare dake Birnin Gwari.

Kokarin da jaridar The Cable ta yi na jin tabakin, Ben Kure shugaban hukumar ta SEMA, ya ci tura.

A ranar 7 ga watan Mayu ne gwamnan jihar, Mallam Nasiru El-rufa’i, ya umarci hukumar ta SEMA da ta gaggauta kai kayan dauki ga mutanen da rikicin ya rutsa da su.

You may also like