Mutane 27 ne suka mutu sakamakon hatsarin da ya afku a kasuwar sayar da kayan wasan wuta a kasar Mekziko.
Rahotanni sun ce, lamarain ya afku a kasuwar da ake sayar da kayayyakin na wasan wuta domin bukukuwan sabuwar shekara.
Sama da mutane 70 ne suka jikkata sakamakon lamarin wanda ya afku a yankin arewa da garin Mekziko da nisan kilomita 20.
A wannan kasuwa dai a shekarun 2005 da 2006 an samu afkuwar lamari makamancin wannan.