Mutane 290,000 Sukayi Rijistar Da Shirin Npower Cikin Kwanaki 3Sama da mutane 290,000 sukayi rijista a shafin yanar gizo na shirin samar da aikin gwamnatin tarayya na Npower.  

Babban mai taimakawa Shugaban kasa kan samar da aiyukan yi,  Afolabi Imoukhuede, ya bada wannan bayanin lokacin da yake ganawa da wadanda suka amfana da shirin a Benin babban birnin jihar Edo. 

A cewarsa mutane 200,000 ne  da suka gama makaranta suka shiga cikin kason farko na shirin yayin da za a kara daukan mutane dubu 300,000  a kaso na biyu. 

  Ya kuma koka kan yadda ake shigar da bayanai ba dai-dai ba yayin da matasan suke shigar da bayanansu a shafin yanar gizon

Imoukhuede yace gwamnati tana kashe naira biliyan 6  a duk wata wajen biyan mutanen da suke karkashin shirin inda yace wannan ba karamin kudi bane. 

Ya kara da cewa a wannan karon za afi bada fifiko ga mutanen da suke zaune a karkara domin maganin kwararowar mutane cikin birane. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like