Mutane 3 Suka Mutu, 17 Suka Jikkata A Harin Kunar Bakin Wake A Sansanin Yan Gudun Na Dolori Dake Maiduguri Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA, ta tabbatar da mutuwar mutane uku a wani harin kunar bakin wake da aka kai sansanin yan gudun hijira na Dolori dake birnin Maiduguri a daren Jiya Lahadi.

Jami’in yada labarai na hukumar dake yankin arewa maso gabas Abdulkadir Idris ya tabbatar da haka a wata sanarwa da yafitar yau Litinin, ya kuma kara da cewa mutane 17 suka jikkata a harin. 

Tun farko kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, yayi ikirarin cewa wata majiya mai tushe a cikin  jami’an tsaro ya fadawa mai kawo musu rahoto cewa jami’an tsaro sun harbe wata yar kunar bakin wake  lokacin da take kokarin shiga sansanin ta wayar da ta kewaye sansanin na yan gudun hijira. 

“Sun harbeta yayin da bam din dake jikinta ta tarwatsata gunduwa-gunduwa, ” a cewar majiyar. 

Majiyar ta kara da cewa wani namiji dan kunar bakin wake, ya samu nasarar shiga sansanin inda ya tayar da bom din dake jikinsa hakan ya jawo mutuwar mutane hudu. 

Majiyar ta kara da cewa “Mutane biyu suka mutu nan take,yayin da ragowar biyun suka mutu a Asibiti. “

You may also like