Mutane 3 sun hallaka, mutane 4 sun jikkata a tashin Bam a jihar Neja


Wani Bam ta tashi a kauyen Gari wanda ke kusa da garin Kontagora a jihar Neja, inda akalla mutane 3 suka rasa rayukansu kuma 4 sun jikkata. Yayinda mazauna garin sukace harin kunar bakin wake ne, yan sanda sunce bahaka bane

Hadarin da ya farune a kasuwan garin ya saukaka ne saboda ba ranar asabar bane ranar kasuwar garin.

Hukumar ya sanda sunce tashin Bam ya auku ne sanadiyar rikon sakeni kashin da wani soja yayi da Bam din. Sojan wanda ya dawo ba da dadewa ba daga Maiduguri wajen yakan yan Boko Haram.

Kakakin hukumar yansanda DSP Bala Elkana, wanda ya tabbatar da labarin yace sunan sojan Private Tanko Damina.

Kakakin hukumar yansanda DSP Bala Elkana, wanda ya tabbatar da labarin yace sunan sojan Private Tanko Damina.

Yace: “ Tanko Damina ya dawo daga Maiduguri kenan. Ya dawo da wasu kananan Bam domin yin alfahari ga kauyawa cewa yayi yaki a Maiduguri. Ya kasance yanan yawo da Bam din cikin kauye.”

Kawai ranan asabar Bam din suka tashi a cikin kasuwa wanda ya kashe shi kanshi Tanko da kuma wasu guda biyu, inda wasu 4 suka jikkata. Mun gode Allah ba ranan kasuwa bane.”

“ Tanko Damina ya dawo da Maiduguri kenan. Ya dawo da wasu kanan Bam domin yin alfahari ga kauyawa cewa yayi yaki a Maiduguri. Ya kasance yanan yawo da Bam din cikin kauye.”

Kawai ranan asabar Bam din suka tashi a cikin kasuwa wanda ya kashe shi kanshi Tanko da kuma wasu guda biyu, inda wasu 4 suka jikkata. Mun gode Allah ba ranar kasuwa bane.”

You may also like