‘Mutane 30 ne suka mutu a Afrika ta Tsakiya’


 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane 30 ne suka mutu a Jamhuriyar Tsakiyar Africa, wasu kuma sama da 57 sun jikkata sakamakon sabon rikici da ya barke a kasar.

Majiyoyin na cewa rikicin ya fara ne a kasuwar garin Kaga Bandoro a lokacin da wasu suka nemi satan injin bada hasken wuta.

Yanzu haka dai akwai Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dubu 12 da aka jibge a wannan kasa.

Tun a shekarar 2013 ake tashin hankali na addinni a kasar wanda ya yi sanadi kujeran gwamnati Francois Bozize.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like