Mutane 30 Sun Mutu A Wani Hatsari Da Yafaru Akan Titin Lagos Zuwa Ibadan 


Wani mummunan hatsari da yafaru akan babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan ya jawo asarar rayukan mutane 30.

Bisi Kazeem, mai magana da yawun hukumar kiyaye hadura ta kasa,FRSC ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN faruwar haka a Abuja. 

 Kazeem yace hatsarin yafaru ne da misalin karfe 8:00 na dare, a dai-dai wurin fasa duwatsu na Elobolo dake kilomita 95 daga bangaren Ibadan na titin. 

A cewarsa mutane 10 sun jikkata a hatsarin wanda ya rutsa da motoci biyu kirar Mazda masu dauke da mutane 40.

” Hatsarin yafaru ne a wani wuri da ake aikin gini kuma yafaru ne saboda saba dokokin hanya da na gudu, “yace. 

Kazeem yace jam’ian hukumar sun kammala aikin ceto a wurin da misalin karfe 2:42 na daren ranar Juma’a. 

Yace tuni aka kai gawarwakin dakin ajiye gawa na asibitin Adeoyo Yemetu dake Ibadan.

You may also like