Mutane 30 sun mutu a wani hatsarin mota a jihar Sokoto


Hoton wata mota da tayi hatsari

Wani mummunan hatsarin mota akan titin Kware zuwa Gwadabawa a jihar Sokoto ya lakume rayukan mutane 30.

Hatsarin da ya haɗa da wata babbar mota da kuma wata mota kirar Toyota Spora wacce aka ce tana dauke da wata amarya da kuma danginta ya faru da misalin karfe 8 na dare.

A tabakin wani shedar gani da ido babban motar na tahowa ne daga karamar hukumar Illela yayin da tayarta ta fashe inda taje ta haɗu da motar dake dauke da amaryar wacce ita kuma ta ke tahowa daga karamar hukumar Kware,wanda hakan ya jawo mutuwar mutane 30.

Da yawa daga cikin mamatan mata ne da kananan yara da kuma tsofaffi.

Amma kuma mai magana da yawun hukumar kiyaye hatsura ta kasa FRSC reshen jihar,Aliyu Kanya, ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a kuma ya lakume rayukan mutane 20 yayin da 12 suka jikkata ciki har da amaryar.

Ya ce wadanda suka jikkata na can na karbar magani a asibiti.

You may also like