A ƙalla mutane 328 ne ake kyautata zaton sun mutu bayan da wata girgizar kasa mai karfin 7.3 a ma’aunin auna karfin girgizar kasa ta faru akan iyakokin ƙasashen Iraqi da Iran.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasar Iran, Isna ya kara adadin yawan mutanen da suka mutu zuwa 328 bayan da aka samu girgizar kasa a lardin yammacin ƙasar da misalin karfe 9:20 agogon kasar,ranar Lahadi.
Masu aikin ceto sun ce adadin mutanen da suka mutu zai iya karuwa domin yanzu masu aikin ceto da jami’an agaji suke isa wuraren da suke da wuyar zuwa.
Lardin Kermanshah shine inda girgizar kasar tafi ƙamari inda har takai da hukumomin sun bada sanarwar zaman makoki na kwana uku.
Sama da mutane 236 suka mutu a garin Sarpo-el zahab dake da tazarar mil goma daga iyakar kasar da Iraqi.
A cewar Kungiyar bada agaji ta Red Crescent dake ƙasar mutane 7000 ne suke buƙatar matsuguni.