Mutane 4000 sun sauya Sheƙa daga APC zuwa PDP a Katsina


PDP-Logo3

Alhaji Nasiru Usman ma’ajin jam’iyar APC  reshen jihar katsina ya sauya sheƙa zuwa jam’iyar adawa ta PDP tare da magoya bayansa mutune 4000.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa ya rawaito cewa masu sauya sheƙar sun Miƙa kansu ga reshen jam’iyar dake ƙaramar hukumar kankiya dake jihar a jiya asabar.
Usman yace sun yanke shawarar sauya sheƙa ne bayan da jam’iyar APC tayi watsi dasu.
” Gaskiya ne na jagoranci mutane da yawa a fafutukar ta tabbatar da nasarar APC a zaben 2015″yace
“Nayi Yakin neman zabe tukuru dan ganin an kayar da dantakarar PDP Musa Nashuni wanda ɗan wannan ƙaramar hukumar ne,inda na tabbatar da cewa ko a ƙauyensu baiyi nasara ba akan Aminu Bello Masari ”
“Amma bayan anyi zabe Masari ya zama gwamna APC tayi watsi da mafi yawancin mu”
Usman yace wasu jigon jamiyar daga ƙaramar hukumar kankiya sun nemi uwar jam’iya ta jiha da ta dakatar tashi saboda wani dalili na ƙashin kansu.
Ya cigaba da cewa yakasance cikin dakatarwa ta tsawon wata 14, duk da cewa reshen jam’iyar na shiyar arewa maso yamma yayi umarnin da a janye dakatarwar bayan da ya shigar da korafi kan cewar dakatarwar ba halattaciya bace.
Usman ya ƙara da cewa sun bar jam’iyar ne tare da mutune 4000 daga mazaɓu goma na ƙaramar hukumar ta kankiya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like