Mutane 45 Ne Suka Kamu da Cutar Amai da Gudawa a Jahar Lagos.


 

 

A jiya Alhamis, gwamnatin jahar Lagos ta sanar da barkewar cutar amai da gudawa a yankin Isolo da ke jahar.

Kwamishinan lafiya na jahar Dr Jide Idris ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya gudanar inda ya tabbatar da rasuwar mutane 6 yayin da kimanin mutane 45 suka kamu. Ya kara da cewa yanzu haka an shwoa kan cutar a jikin mutane 36 a asibitoci a fadin jahar yayin da ake yiwa mutane 4 kokari.

Kwamishinan ya bayyana cewa sun gano silar barkewar cutar wani abincin gargajiya ne da ake kira Abacha da kuma ruwan rijiya. Ya ce binciken da suka yi akan ruwan da abincin a hukumar bincike ya nuna cewa tabbas Abacha na dauke da kawar cutar da ke haifar da amai da gudawa, haka kuma ruwan rijiyoyi biyu a yankin na dauke da kwayar cutar.

Karanta Wannan:Cutar Amai Da Gudawa Ta Barke a Jahar Lagos

Yayi kira ga mutanen jahar da su tsaftace muhallinsu su kuma jimirci wanke hannayensu da ruwa da sabulu a-kai a-kai.

You may also like