Kungiyar da ke sa ido kan hakkin dan Adam a Syria ta ce, fiye da ‘yan tawaye da dakarun gwamnatin kasar 500 ne suka rasa rayukansu a cikin mako guda da aka shafe ana gwabza yaki da nufin karbe birnin Aleppo daga hannun mayakan jihadi.
Shugaban kungiyar Rami Abdel Rahman ya bayyna cewa, akalla fafaren hula 130 ne suma suka mutu sakamakon farmakin da ‘yan tawayen suka kaddamar a yankunan da dakarun gwamnati ke rike da su.
A bangare guda, ‘yan tawayen na Syria sun ce, sun wargaza kawanyar makwanni uku da dakarun gwamnatin suka yi musu a birnin na Aleppo, lamarin da ya dagule ayyukan dakarun da ke samun goyon bayan Rasha.