Mutane 56 Sun Mutu Sakamakon Barkewar Wani Sabon Rikici A Sudan Ta Kudu


 

Rahotanni daga kasar Sudan ta Kudu sun bayyana cewar wani adadi mai yawa na mutanen kasar sun rasa rayukansu sakamakon wani musayen wuta da ya faru tsakanin sojojin gwamnati da na ‘yan tawaye a kusa da garin Malakal lokacin da ‘yan tawayen suka yi kokarin kwace garin.

Kakakin sojan Sudan  ta  Kudun Lul Ruai Koang ya bayyana cewar dakarun ‘yan  tawayen sun kai hari ne kan sansanonin sojojin gwamnatin, inda ya ce sojojin gwamnatin sun sami nasarar fatattakar ‘yan tawayen da kuma kashe wani adadi mai yawa na su, wanda a cewar kakakin sun kai ‘yan tawaye 56.

Tun da fari dai mataimakin kakakin sojojin ‘yan tawayen Dickson Gatluak ya sanar da cewa dakarun na su sun kwace garin wasu garuruwa guda biyu da suke kusa da garin na Malakal wanda shi ma za su kwato shi; lamarin da kakakin sojan gwamantin Sudan ta Kudun ya musanta yana mai cewa garin yana hannun dakarun na su kuma tuni suka fatattakin ‘yan tawayen.

Kamfanin dillancin labaran Reuters dai yace dan rahotonsu ya ga gawawwakin mutane da yawa a wajen da kuma wani gini na sojin da aka kona.

You may also like