Mutane 6 aka harbe har lahira a wani sabon hari a yankin kudancin Kaduna


Aƙalla mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wannan sabon hari da wasu yan bindiga da ake kyautata zaton Fulani makiyaya ne suka kai a kauyen Anguwan Mailafiya a yankin masarautar  Gwong dake karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna.

Harin na baya bayannan ya faru ne kasa da sa’o’i 48 bayan da wasu yan bindiga suka kai hari kan wasu masu ibada a wata coci dake  al’ummar Nindem.

Ya zuwa yanzu babu wani cikakken bayani akan harin amma an ce yan bindigar sun dirarwa kauyen da misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi.

Da yake tsokaci akan harin Shehu Garba wakilin mazabar Jema’a/Sanga a majalisar wakilai ta tarayya ya yi kira ga gwamnan jihar, Mallam Nasiru El-Rufai da kuma hukumomin tsaro kan suyi maganin matsalar kafin ta rikide zuwa wani babban tashin hankali.

“Cikin kaduwa da damuwa na samu labarin hari kan ƙauyen Nindem dake masarautar Godogodo  da misalin ƙarfe 10:00 na dare ranar Juma’a 22 ga watan Disamba ,”sanarwar tace.

“Mutane huɗu aka kashe goma kuma suka samu mummunan rauni.

“Yayin da muke cikin jimamin wadanda suka mutu a Nindem, da misalin karfe goma na daren ranar Lahadi jami’an tsaro suka samu kiran kai daukin gaggawa kan wani sabon harin da yafaru akan ƙauyen Unguwar Mailafiya dake masarautar Gwong.

“Zuwa safiyar ranar kirsimeti mutane 6 aka tabbatar da sun mutu da suka hada da yaro mai shekaru 6 yayin da wasu da dama kuma suka jikkata,”dan majalisar wakilai ta tarayya ya fadi haka cikin sanarwar da yafitar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like