Mutane 6 Sun Mutu Bayan Da Kwale-kwalen Da Suke Ciki Ya Kife A Jihar Taraba 


A kalla mutane 6 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka bace a cikin ruwa wadanda  galibinsu manoma bayan da jirgin kwale-kwalen da suke ciki ya rabe biyu a kogin Benue a karamar hukumar Gassol ta jihar Taraba.

Jaridar Premium times ta gano cewa tuni aka garzaya da mutane hudun da aka samu nasarar ceto su zuwa Asibiti.

Jirgin dake dauke da fasinjoji da ba’a gama tantance su  ba yawancinsu manoma ne daga garin Mutum Biyu ya rabe gida biyu ne bayan da yaci karo da wani abu a cikin ruwan. 

 Shugaban karamar hukumar Gassol Yahuza Yayau yace adadin mutanen da suka mutu zai iya karuwa saboda masunta da sauran masu ceto na cigaba da neman mutanen da abin ya rutsa dasu. 

” Muna samun rahoton faruwar lamarin mun kira masunta domin su taimaka wajen ceto fasinjoji da suka bace.

 “An fada min cewa an gano gawarwakin mutane shida an kuma samu nasarar ceto mutane hudu yayin da ake cigaba da aikin ceto mutanen,” a cewar shugaban.

Wani mazaunin yankin dake aikin ceto mutanen a hirar da akayi dashi ta wayar tarho yace  ” Dukkanin fasinjoji dake cikin jirgin sun bace, amma yayin da ake cigaba da aikin ceto an gano gawarwakin mutane shida yayin da mutane hudu da suke da ransu aka garzaya dasu zuwa asibiti.”


Like it? Share with your friends!

0

You may also like