Mutane 61 sun mutu a hatsarin jirgin sama a kasar Iran


Jirgin saman kamfanin Aseman, na ƙasar Iran dake jigilar fasinjoji ya yi hatsari a ranar Lahadi inda dukkanin mutane 61 dake cikin  jirgin suka mutu.

Jirgin ya yi hatsari a wani yanki mai tsaunuka mintuna 50 bayan tashinsa daga filin jirgin saman Tehran, babban birnin ƙasar, kamfanin dillancin labarai na ISNA ya jiwo daga bakin, Mojtaba Khaledi mai magana da yawun sashen kai daukin gaggawa na kasar.

Gidan Talabijin na ƙasar ya jiwo mai magana da yawun kamfanin na tabbatar da mutuwar mutane.

“Mai magana da yawun jirgin Aseman na cewa abin takaici dukkanin fasinjojin dake ciki sun mutu.”

Kasar  Iran ta fuskanci faduwar jiragen sama da dama a yan shekaru gommai da suka wuce.

Tehran ta ce takum-kumin da kasar Amurka ta saka mata ya ɗaɗe yana hanata sayan sababbin jiragen da kuma sauran kayayyakin gyaransu.

You may also like