Mutane 7 sun mutu a rikicin Kaduna


Aƙalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a wani rikici da ya ɓalle a Kasuwar Magani dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Mutane da dama sun samu raunuka ya yin da aka kona gidaje masu yawa a rikicin.

Wata majiya a jami’an tsaro ta bayyana cewa  gawarwakin mutane bakwai aka ƙidaya bayan da jami’an tsaro suka isa wurin.

Ba a san dalilin da ya haddasa rikicin ba sai dai wasu na cewa rikicin yana da alaka da addini.
Matafiya dake bin babbar hanyar da ta haɗa jihohin Nasarawa, Plateau da kuma Benue  da kuma kudancin Kaduna sun tsaya na tsawon awanni saboda babu zirga-zirgar ababen hawa a lokacin da ake tsaka da rikicin.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, Aliyu Mukhtar ya ce tuni aka shawo kan lamarin.

You may also like