Mutane 7 sun rasa rayukansu,136 kuma sun ɓace a hatsarin jirgin ruwan da yafaru a jihar Kebbi


boat

A ƙalla mutane 7 suka mutu wasu bakwai kuma suna asibiti a ƙaramar hukumar Ngaski dake jihar Kebbi, bayan da jirgin ruwan da suke ciki mai ɗauke da mutane 150 yayi hatsari a kogin Neje akan hanyarsa ta dawowa daga kasuwar Malali.

Jami’in tsare-tsare na hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa NEMA mai kula da jihohin Sokoto Kebbi da Zamfara Alhaji Sulaiman Muhammad ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a Ngaski yau Asabar.

Yace ana cigaba da ƙoƙari tsakanin masunta da kuma jami’an hukumar kula da hanyoyin ruwa ta ƙasa NIWA don ganin an ceto fasinjojin da suka ɓace.

“Lokacin da muka samu faruwar hatsarin mun kira hukumar kula da hanyoyin ruwa ta ƙasa don ta taimaka a ceto mutane”

“ dukkanin mutanen dake cikin jirgin sun ɓace, amma  daka fara nema da kuma ceton mutanen an samu nasarar samun mutane 14, 7 sun mutu  7 kuma suna babban asibitin Ngaski suna karɓar Magani”

Hatsarin dai yafaru ne sakamakon cin karo da itace da jirgin yayi a cikin ruwan wanda hakan ya janyo nutsewarsa.

Tafiyar sa’a biyu ce daga wurin da hatsarin ya faru zuwa ƙaramar hukumar Ngaski


Like it? Share with your friends!

0

You may also like