Mutane 700,000 Suka Nemi Aikin FIRS Mai Gurabe 500


 

Hukumar tara haraji ta kasa FIRS ta ce masu neman aiki gudaiye da 700,000 ne suka amsa gayyatar ta na neman aiki na cike gurabe 500 da ta tallata.

Shugaban Hukumar Tunde Fowler shi ya bayyana haka a ranar Larabar da ta gabata a Abuja yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan sauraron koke-koken jama’a.

Hukumar yada labarai ta Nijeriya ta rahoto cewa shugaban hukumar ta FIRS ya bayyana ne a gaban kwamitin na majalisa a sakamakon koke koken da wasu daga cikin masu neman aiki ke yi na cewar an ware su daga tantancewar daukan aikin.

Ya ce sama da mutane2, 000 daga cikin masu neman aikin na da digiri daraja ta daya (1st class), kuma dukkansu sun cancanci a dauke su.

Sai dai ya kara da cewa hukumar ba za ta iya daukan mutane fiye da 500 ba, amma za ta tabbatar cewa tsarin da aka bi wajen daukan aikin akwai gaskiya a ciki.

Wannan lamari dai ya nuna kururu yadda rashin aikin yi ya yi wa matasan Nijeriya katutu, duk da cewa Nijeriya ita ce kasar da ta fi kowacce kasa a nahiyar Afirka karfin tattalin arziki.

You may also like