Mutane 8, Sun Rasa Rayukansu A Jihar Benue, A Wani Hari Da Ake Zargin Fulani Da Kaiwa


A kalla mutane 8 ne suka rasa rayukansu bayan wani da hari da ake zargin Fulani makiyaya da kaiwa, akan kauyuka biyu dake karamar Hukumar Logo ta jihar Benue. 

Mai magana da yawun rundunar yan sandar jihar,Moses Yamu, ya tabbatar da faruwar kai harin a wata sanarwa da yafitar jiya Litinin. 

Yamu, yace harin akan kauyuka Akaa da Tse-orlalu, dake al’umomin Mbamar da Ugondo ana zargin Fulani da kaiwa. 

Yace haryanzu yan sanda basu gano dalilin kai harin ba, amma tuni aka Kai jami’an tsaro yankin domin dawo da zaman Lafiya. 

Yace maharan sun mamaye kauyukan, suka kuma  kashe mutane 8, tare da jikkata wasu da dama. 

Wani shaidar gani da ido, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN cewa, maharan sun shigo ne daga jihar Taraba me makotaka da jihar ta Benue.

“sun fara kai hari kan kauyen Akaa, kafin su karasa kauyen Orlalu mai makotaka dashi,”yace

Shaidar gani da idon wanda ya nemi a sakaya sunansa yace mutane da dama sun bace a kauyukan.

Harin makiyaya akan kauyuka a jihar Benue ba bakon abu bane, matsala ce da take yawan faruwa.

Abin jira a gani shine, ko tayaya hukumomi zasu kawo karshen asarar rayuka da kuma dukiyoyi a jihar.

You may also like