Mutane 90 Sun Mutu Bayan Fashewar Wani Babban Bom A Kabul Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Gani, yayi Allah wadai da harin bom din da aka kai babban birnin kasar  Kabul, da ya kashe mutane 90 tare da jikkata wasu da dama. 

Fashewar mai karfin gaske da jami’an gwamnati suka bayyana a matsayin fashewar wani bom mafi girma da ta taba samun birnin.

A cewar Najib Danish, mataimakin mai magana da yawun  ma’aikatar cikin gidan kasar yace an boye bom din ne a cikin wata mota dake aikin gyaran bututun dake daukar dagwalon bandakin gidajen birnin.

Fashewar ta haifar da wani rami mai tsawon mita 5  kusa da dandalin Zanbaq dake yankin Wazir Akbar Khan, inda ofisoshin gwamnati suke da kuma na jakadancin kasashen waje. 

 Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin sai dai magana da yawun kungiyar Taliban Zabihulla Mujahid, ya shaidawa gidan Talabijin na Aljazeera cewa kungiyarsu bata da hannu akai harin .

Hukumar leken asirin kasar ta Afghanistan ta dora alhakin kai harin akan kungiyar Haqqani mai alaka da Taliban da kuma makociyar kasar Pakistan.

“kungiyar Haqqani sun shirya harin na ranar Laraba  tare da taimako da kuma hadin kan hukumar leken asirin kasar Pakistan (ISI),” a cewar sanarwar da hukumar leken asirin ta fitar.

Afghanistan dai ta dade tana zargin kasar Pakistan da boye mayakan Haqqani da shugabannin Taliban da sauran mayakan dake yaki da gwamnatin Kabul a cikin kasarta, zargin da Pakistan take musaltawa. 

You may also like