Mutane biyar sun mutu a harin kunar bakin wake da aka kai wani Masallaci dake Bama


Akalla mutane biyar aka tabbatar da sun mutu a wani harin kunar bakin wake da wasu yan mata suka kai garin Bama dake jihar Borno.

Masu ibada da dama ne suka jikkata a harin kunar bakin waken da aka kai da misalin 5:30 na safe.

Ali Abatcha wani ma’aikacin hukumar tsaro ta NSCDC ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar The Cable inda yace harin na kunar bakin wake ne.

Abatcha ya ce yan kunar bakin wake mata biyu su ne suka shiga cikin masallacin lokacin da ake gabatar da sallar Asuba.

“Wadanda suka jikkata an garzaya da su asibitin sojoji dake Bama ya yin da wasu daga cikin mamatan da iyalansu suka gane su aka binne su kamar yadda shari’ar Muslunci ta tanada,” ya ce.

Ibrahim Kachalla daya daga cikin yan uwan wadanda suka mutu ya ce biyu daga cikin yan uwansa sun rasa rayukansu a harin.

“Munji fashewar wani abu mai kara a lokacin muna tsaka da gabatar da Sallah. Fashewar mai kara ce sosai dukkaninmu mun san cewa wani mummunan ya faru,” ya ce.

“Da muka doshi gurin akwai gawarwaki watse a ko ina ciki har da na yan uwana su biyu.”


Like it? Share with your friends!

0

You may also like