Mutane biyu aka kama ɗauke da bindigogi a tashar motar Gwagwalada


Mutane biyu da ake zargin yan fashi da makami ne dauke da bindiga aka kama  a tashar motar Gwagwalada dake Abuja.

Wani sheda mai suna Daniel yace an kama mutanen ne da misalin karfe 11 na safe lokacin da  suka zo hawa mota a tashar Wazobia dake kan titin Abuja zuwa Lokoja.

Ya ce mutane biyun da ake zargi sun boye bindigogin a cikin rigunansu, daya daga cikin ma’aikatan tashar motar dake zuba fasinja a wata mota ne ya lura da bindigogin yayin da daya daga cikin mutanen ke ƙoƙarin shiga  motar.

Ma’aikacin ya ankarar da jami’an yan’sanda inda aka tura jami’ai cikin farin kaya suka zo suka kama su.

Tuni wasu mutane suka shiga dukan mutanen biyu kafin bayyanar jami’an yansanda har ta kai ga sun samu rauni.

Da aka tuntubi baturen yan’sanda na Gwarinpa, CSP David Kolo ya  tabbatar da kama mutanen biyu. 

You may also like