Mutane biyu sun mutu a hatsarin mota a Abaji


Yaro dan shekara 6 da kuma wani mai tafiya a kasa da aka bayyana da suna Abdul sun mutu a wani hatsarin mota da safiyar ranar Alhamis a garin Abaji dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa wasu ƙarin mutane shida ciki har da yara biyu sun jikkata a hatsarin kuma jami’an hukumar kiyaye hatsura ta kasa FRSC sun garzaya da su Asibiti.

Wani sheda da yaganewa idonsa abin da ya faru ya ce hatsarin yafaru ne lokacin da wata mota kirar Honda Academy dake tahowa daga Abuja ta kade mutumin da yake tafiya a kasa lokacin da yake tsallaka titin.

Yace direban yayi kokarin kaucewa wata motar tirela da kawai ta tsaya a gabansa inda motar ta kwace ta dungura tare da kashe wani yaronl dake zaune a ciki.

Faruwar hatsari akan hanyar Abuja zuwa Lokaja  abu bane da yake nema ya zama ruwan dare, duk da ƙoƙarin da hukumomin suka ce suna yi na shawo kan lamarin.

You may also like