Mutane biyu sun mutu a wani rikicin tsakanin yan shi’a da yan sanda a Kano


Wani jigo a kungiyar yan uwa musulmi dake Najeriya wacce akafi sani da kungiyar shi’a da kuma wata mace yar kungiyar na daga cikin mutanen da ake zargin yan sandan kwantar da tarzoma suka kashe a Kano.

Rikicin ya fara ne bayan da jami’an yan sandan suka yi yunkurin hana su tattakin da suka saba yi duk shekara da ake kira arba’in.

Wani da ya ganewa idonsa abinda ya faru ya ce lamarin ya faru ne adai-dai kasan gadar Ado Bayero wacce akafi sani da gadar Lado.

Ana  zargin yan sandan da yin amfani da  barkonon tsohuwa da kuma harsashi wajen dakatar yan kungiyar ta shi’a.

Mutane da dama ne suka samu raunuka a artabun da aka yi.

Jihar Kano na daga cikin jihohin da suka haramta kungiyar ta yan shi’a.

Har ya zuwa yanzu rundunar yan sanda ta Kano ba ta ce komai ba game da rikicin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like