Mutane da dama sun hallaka a Habasha


Gwamnatin Habasha ta tabbatar da cewa wasu mutane sun hallaka sakamakon matakin da jami’an tsaro suka dauka akan masu zanga-zanga.

Äthiopische Volksgruppe der Oromos Protest (Getty Images/AFP)

Gwamnatin kasar Habasha ta tabbatar a wannan Lahadin cewa wasu mutane sun hallaka yayin da wasu da dama suka samu raunika, sakamakon turmutsitsin da aka samu lokacin da ‘yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye, yayin gangamin ‘yan adawa. Amma gwamnatin ba ta bayyana wasu alkaluma na mutanen da lamarin ya ritsa da su ba.

‘Yan adawa sun ce kimanin mutane 50 ne suka hallaka sakamakon matakin na ‘yan sanda kan masu adawa da gwamnati. Rahotanni sun ce lamarin dai ya afku ne a kusa da birnin Addis Ababa fadar gwamnatin kasar ta Habasha yayin da ‘yan kabilar Oromo suke wata al’ada ta shekara-shekara a karshen damina. Masu gudanar da bukukuwan sun yi ta nuna wata alama da aka saba yi wadda ke nuni da yin adawa da gwamnati.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like