Mutane da yawa sun mutu cikin jerin hare-haren kunar bakin wake a  birnin Maiduguri


Mutane da yawa ake fargabar sun rasa rayukansu wasu da dama kuma suka jikkata a wani jerin harin bama-bamai a birnin Maiduguri.

Fashewar bam din ta faru ne da misalin karfe 8:40 na dare a yankin Garejin Muna a karamar hukumar Jere dake cikin birnin Maiduguri.

A cewar wata majiya ta jami’an tsaron sa kai da ake kira Civilian JTF wani dan kunar bakin wake ne ya tashi bam din dake jikinsa a tashar motoci ta Muna inda ya kashe mutane masu yawa tare da  jikkata wasu da dama.

Hari na biyu ya faru ne cikin sansanin yan gudun hijira inda mutane 10 suka jikkata, ya yin da hari na uku ya faru akan titin Gamboru Ngala.

” Ya zuwa yanzu,  bayanan da aka samu na nuni da cewa dan kunar bakin wake na farko da ya tada bam a kofar shiga tashar mota ta Muna, ya kashe mutane 13 tare da raunata wasu 6, ya yin  da dan kunar bakin wake na biyu a cikin sansanin yan gudun hijira ya raunata mutane 10,”  a cewar majiyar ta CJTF a hirar da jaridar Daily Trust ta yi dashi ta wayar tarho.

Wani ma’aikacin ceto ya ce adadin mutanen da suka mutu zai iya zarce haka, saboda yankin Garejin na Muna yana da hatsarin gaske ga ma’aikatan agaji da daddare.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like