Mutane da yawa sun rasa rayukansu a wani rikici tsakanin masu haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da kuma jami’an yan’sanda a wurin haƙar ma’adanai na Mayo Sine dake hayin Mambila a jihar Taraba.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa lamarin yafaru da yammacin ranar Alhamis, lokacin da wasu tawagar jami’an yan’sanda dauke da makamai suka dira wurin domin fatattakar mutane amma sai suka fuskanci turjiya.
Akwai kimanin masu hakar ma’adanai 10500 da suka fito daga ƙasashen yankin Afrika ta yamma inda suke gudanar da haƙar ma’adanai a wurin ba bisa ka’ida ba fiye da shekaru goma.
Jaridar ta gano cewa yan’sandan suna isa wurin suka fara lalata gidajen da mutanen suke kwana tare da kwace kayayyakin da suke amfani dasu wajen hako duwatsu masu daraja a wurin.
Tun da fari gurin da mutanen suke haƙar ma’adanan an bawa wani kamfanin kasar waje damar ya haki ma’adanai a wurin amma mutanen suka ki tashi har ta kai aka tura jami’an tsaro.
Abin da yan’sandan suka yi ne ya harzuka masu haƙar ma’adanan inda suka kori yan sandan tare da lalata wasu kayayyaki na kamfanin hakar ma’adanan.
A ƙoƙarin da suka yi na tarwatsa fusatattun masu hakar ma’adanan yan’sanda sun bude wuta inda suka kashe wasu da yawa daga cikinsu.