An bayyana cewa, tun bayan fara rikicin kungiyar ta’adda ta Boko Haram an kashe mutane kimanin dubu 100 sakamakon hare-haren kungiyar da kuma arangamar da ta ke yi da sojoji a Najeriya.
Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso-gabashin Najeriya Kashim Shettima ne ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2009 zuwa yau an kashe mutane dubu 100 a rkicin na Boko Haram.
Shettima ya ce, a kasar Afirka ta Kudu da aka dauki shekaru 21 ana yakin nuna wriyar launin fata an kashe mutane dubu 21 ne kawai, amma kuma Boko Haram a cikin shekaru 7 ta yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 100 da mafi yawansu mata ne.
Kakakin gwamna Shettima Isa Gusau ya sanar da cewa, mafi yawan wadanda aka kashe sun fito ne daga wajen jihar ta Borno.
Ya ce, sakamakon rikici mutane miliyan 2.1 sun rasa matsugunansu, mata dubu 55 sun rasa mazajensu inda yara kanana dubu 52 suka zama marayu.