Ma’aikatan bayar da agaji huɗu dake aiki da shirin samar da abinci na majalisar dinkin duniya, akayi garkuwa da su a jihar Borno.
Shirin na samar da abinci na duniya, wani bangare ne na majalisar dinkin duniya dake samar da abinci ga mutanen da rikici ya shafa ko kuma fari.
A wani sako da shirin ya aikewa da jaridar Premium Times, ya ce an kai harin kwanton bauna kan motocinsu dauke da kayan abinci dake samun rakiyar sojoji akan hanyar su ta kai abinci ga sansanin yan gudun hijira dake garkn Ngala a ranar Asabar.
Mutane huɗu aka tabbatar da mutuwarsu yayin kai harin yayin da ake tunanin yan bindigar da ake kyautata zaton ya’yan kungiyar Boko Haram ne sun yi awon gaba da wasu mutane huɗu.
A cewar jami’in sadarwa na shirin dake Maiduguri, Adedeji Ademigbuji ya ce biyu da ga cikin mutanen da aka kashe direban mota ne da kuma mai taimaka masa.
Amma wasu majiyoyi dake da masaniyar harin sun tabbatarwa da jaridar Premium Times cewa yan bindigar sun sace wasu mutane uku wadanda suka tuka motar zuwa wani guri da ya zuwa yanzu ba a iya ganowa ba.