Kakakin rundunar sojin Masar ya sanar da mutuwar ‘yan ta’adda 23 da jami’an tsaron kasar 2 a dauki ba dadin da aka yi tsakanin bangarorin biyu a sassa daban daban na lardin Tsibirin Sina na Arewacin kasar.
Kakakin rundunar sojin Masar Muhammad Samir a yammacin jiya Laraba ya fitar da sanarwar cewa: Jami’an tsaron Masar sun harbe wasu gungun ‘yan ta’adda biyar har lahira a yankin Jihad Abu-Difla da ke garin Arisha cibiyar lardin Tsibirin Sina na kasar.
Samir ya kara da cewa: Jami’an tsaron na Masar sun kashe wasu gungun ‘yan ta’adda takwas da suke kokarin kai hari da wata mota da suka makare da bama-bamai a wani wajen bincike da ke garin na Arisha.
Har ila yau jami’an tsaron Masar sun yi dauki ba dadi da wasu gungun ‘yan ta’adda a garin Sheikh Zuwaid da ke lardin na Tsibirin Sina, inda suka kashe ‘yan ta’adda shida. Yayin da a wata musayar wata ta daban tsakanin jami’an tsaron na Masar da wasu gungun ‘yan ta’adda ta lashe rayukan ‘yan ta’adda hudu da na jami’an tsaro biyu tare da jikkatan wasu takwas na daban daga cikin jami’an tsaron kasar.