Mutane uku sun mutu bayan da wata falwayar wutar lantarki ta fado kan wata mota Lagos


A kalla mutane uku ne ake fargabar sun mutu  wasu da dama kuma suka jikkata da safiyar ranar Laraba, bayan  da wata falwayar wutar lantarki ta fado kan wata motar haya.

Hatsarin ya faru ne a tsakanin Ilasa da Itire  dake jihar.

Masu ceto da suka haɗa da y’ansanda da suka fito daga ofishin y’ansanda dake Ilasa da Itire, jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos da kuma yankwanakwana duk sun kasance a wurin domin shawo kan lamarin.

“Mutane da yawa sun jikkata uku kuma suka mutu, wata falwaya ce ta haɗa hatsarin bayam ta fado kan wata mota dake tafiya . Jami’an yan sandan mu suna,” a cewar wata majiyar yan sanda. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like