Mutane uku sun mutu dalilin batakashi tsakanin Hausawa da Igbos a Imo


IGBO

Hukumar yan sanda na jihar Imo sunce kimamin mutane uku ne aka kashe a yayin karon batakashi tsakanin Hausawa da Igbo, hukumar yad’da  labaria na kasa (NAN), sunce Mata biyu da  na miji daya aka kashe a wani kauye  a karamar hukumar ‘Ideato’ ranar juma’a anan. DSP Andrew Enwerem, me magana da yawun yansandan jihar ya bada tabacin faruwan alamarin a yayin magana da hukumar NAN ranar juma’an nan a Owerri,yace raguwan mutanen da abu yashafa sun ji raunuka.

Enwerem ya bayana cewa wani bahaushen ne ya kashe wata yarinya da wata mata daga bisani ya kashe kansa, ya kara da cewa  dalilin haka samarin garin suka far wa mutane. wanda dalilin haka ne yayi sanadiyar yiwa mutane da dama raunika. A cewar Enwerem, bayanan fadan ya iske hedkwantar yansandan jihar batare da bata lokaci ba kuma kwamisionan yansandan jihar ya baza dakaru wajen sayar  da rigimar, kuma haryanzu yansandan suna kokari gano waye kuma me dalilin da yasa bahaushen mutumin yin wannan mumunar ika-ika.

 

 

 

You may also like